SANARWA..... DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMIDUMINSU SAI A SHIGA. https://www.alkaryarhausa.blogspot.com
Abubuwan da ake bukata
1. Madarar gari
2. Danya ko busashsshiyar citta (a daka/kirba)
3. Fulawa
4. Lemon tsami
5. Dafaffiyar alkama ko shinkafa
6. Sikari da yar zuma
7. Kaninfari da citta mai yatsu (a daka)
Yadda ake Hadawa
* Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba kaminfari da citta a ciki sai ki
bari ya tafaso
* Idan ya tafasa sai ki kawo dafaffiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya
* Sai ki kawo fulawa ki kwabata da ruwa ki ringa zubawa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
* Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki
* Sai ki zuba sikari da yar Zuma in kina bukata a sha
No comments:
Post a Comment