Wednesday, 4 April 2018

MIYAR EDIKA IKONG

Abin Sani

Miyar Edikan Ikong ba miyar Hausawa ba ce, sai dai miya ce da
al’ummar Hausawa ya kamata ta mika hannu ta karba, ta runguma
saboda armashin miyar a baki da kuma dimbin alfanunta ga lafiya.
Miyar Edikang Ikong miyar kabilar Efik ce. Ita kuwa kabilar Efik
tushensu na jihohin Cross River da Akwa Ibom a kudancin Nijeriya.
Su ne kabilar da ake kira da Calabar saboda wani adadi mai yawa na
Efik sun fito ne daga garin Calabar, babban birnin jihar Cross River. Ga
dai yadda ake shirya miyar ta Edikang Ikong:

Abubuwan da ake bukatar

* Alayyahu
* Ganyen Ugu
* Ganyen Gurai (water leaves)
* Manja
* Naman sa
* Ganda
* Kayan ciki
* Cray fish
* Hanta
* Busasshen kifi
* Albasa
* Attaruhu
* Gishiri
* Sinadarin Dandano
* Curry
* Thyme
* Citta da sauran kayan kamshi
* Fafarnuwa

Yadda Ake Girka Miyar Edikang Ikong

1. Za ki sami tukunya, ki zuba, namanki, da gandarki, da kayan ciki (bayan kin wanke su da kyau). Ki sa musu albasa isasshe, da thyme, curry, da sinadarin dandano da gishiri, citta, da tafarnuwa. Ki zuba wadataccen ruwan da zai dafa su, ki aza bisa wuta ki barsu su
dahu sosai. Bayan kin tabbatar da dahuwarsu
2. Sai ki sami busasshen kifinki, ki wanke shi tsaf,  wurin wankewar ki dan saka gishiri, bayan kin yi wankewar farko, sai ki saka masa ruwan zafi sannan ki tsane shi, sai ki
sa a cikin naman ki da ya dahu, ki bar shi ya yi kamar minting 8.
3. Bayan ruwan tafasan namanki ya yi kasa sosai, don miyar ba a cika wa miyar Edikang Ikong ruwa, sai ki zuba jajjagaggen taruhu, cray fish, da kuma manja, sa’annan ki jujjuya, sai ki barshi ya dahu na kamar minti 5, sannan ki saka sinadarin dandano.
4. Sai ki dauko ganyen alayyahunki da na water leaves da tuni dama kin yanka kin wanke kin kuma tsane, ki zuba akan hadin miyar. Sai ki tona miyar ta yadda ganyen da kayan hadin za su hautsina sosai, sai ki barshi na ‘yan mintina.
5. Bayan ‘yan mintina sai ki zuba ganyen Ugunki, ki jujjuya, zaki ga miyan duka ya kame babu ruwan miya a cikin sa sai dan kadan, sai ki dan bashi mintina ki rage wutan yadda ganyen za su turaru.
6. Sai ki sauke, Za a iya ci da Sakwara, tuwo, teba, farar shinkafa da dai sauransu

A lura: Za ki iya dafa gandarki daban tunda shi yana da tauri, wasu kuma suna tafasa dukkan naman da zasu yi amfani dashi. Miyar bata bukatar kayan miya kamar yadda muke yin miyarmu, taruhu 3 zuwa 5 ya isa. Sannan miya ce da ke da bukatar nama isasshe. Miya ce mai mutukar kara lafiya saboda ganyayykin da aka yi amfani da su.

No comments:

Post a Comment