Saturday, 7 April 2018
MIYAR SHUWAKA
Abubuwan da ake bukata
1. Makani
2. Ganyen shuwaka
3. Naman sa da kaza da kayan ciki da harshen sa da busashshen kifi
4. Daddawa
5. Attaruhu da tattasai
6. Man ja
7. Dakakken karafish
8. Gishiri da dunkulen knorr
9. Albasa
Yadda ake hadawa
1. Ki wanke kayan ciki sosai da harshen sa, ki yanka albasa da gishiri da dunkulen knorr ki zuba akai, ki zuba ruwa ki rufe ki dora akan wuta.
2. Kayan ciki yana da daukar lokaci kafin ya dahu. Idan kuma kina da (pressure cooker) shi kenan, nan da nan za ki ga ya dahu.
3. Busashshen kifinki kuma ki wanke sosai ki tsame ki ajiye a gefe daya.
4. Ki dafa nama da kaza, shi ma ki yanka albasa, ki zuba gishiri da dunkulen knorr. Amma daban-daban za ki dafa su, domin kaza ta fi nama saurin dahuwa musamman idan naman sa ne. Ka da ki zuba ruwa da yawa, kadan din ruwan naman da zaki samu ya fi mai yawa din nan. Sai dai idan kin ga naman bai dahu ba kina iya kara ruwa .Saboda kadan din ya fi zaki da amfani a jiki.
5. Idan naman ya kusa dahuwa sai ki zuba busashshen kifin da ki ka wanke su karasa dahuwa tare. Ki wanke makaninki ki dafa shi a cikin ruwa, idan ya dahu sai ki sauke ki bare
bawon ki daka shi a turmi. Idan kuma kina da dan karamin injin nika wato (blender) sai ki zuba shi a cikin (blender) ki zuba ruwa. Amma ki dan marmasa makanin da hannu saboda ya yi saukin nukuwa a cikin blender din.
6. A cikin babbar tukunya ki kawo kayan cikin da harshen sa da busashshen kifi da kaza da nama da kika dafa ki zuba a cikin babbar tukunya, ki kawo markadadden tattasai da attaruhu ki zuba akai, ki zuba manja da daddawa da gishiri da dunkulen knorr ki juya, ki barshi kamar minti biyar zuwa minti takwas. Idan kika ji kamshin daddawar ya fara tashi sai ki zuba wannan makanin da kika nika, da farko za ki ga ya fara tashi , idan ya yi ‘yan mintuna kuma sai ki ga ya ,lafa ya fara yauki.
7. Ki juya sosai ki kawo karafish ki zuba a ciki. Karafish yana saka miya ta yi kauri. Idan kin ga miyar ta yi kauri sai ki kara ruwan nama, idan kumabaki da shi kina iya kara ruwa. Wasu suna son miyar shuwakarsu da kauri a yayin da wasu suke sonta da ruwa-ruwa. A gefe kuma kin riga kin wanke shuwakarki sosai da ruwan zafi , idan baki son dacinta da yawa sai ki dafata da kanwa da gishiri, dacin zai ragu sosai, idan ba haka ba kuwa sai kiyi ta wanke shuwakar har sai ta daina wannan kumfa-kumfar kuma koren ya ragu. Ki yankata yadda kike so, wasu suna son su yanka ganyen da girma domin suna jin dadin taunawa, yayin da wasu kuma suke yanka ganyen kananu sosai.
8. Ki rage wuta sosai ki zuba ganyen shuwakar a ciki, ki bar ganyen ya dahu. Ganyen shuwaka ya fi alaiyahu tauri, saboda haka ki bar shi zuwa minti takwas ko goma. Idan kin ga ya yi kauri da yawa sai ki kara ruwa. Ki dandana ki ji komai ya ji.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment