Abubuwan da ake bukata
1. Tsakin Masara (barjajjiyar masara)
2. Zogale ko Alayyaho
3. Attaruhu
4. Albasa
5. Man gyada
6. Dakakkiyar gyada
7. Maggi
8. Kayan kanshi
9. Gishiri
Yanda ake hadawa
1. Da farko uwargida za ki wanke tsakin masararkii ya fita tas, sai ki tsane shi a mararaki.
2. Idan ya tsane sai ki zuba ruwa a tukunyar dambu ko tukunya mai dan zurfi, sai ki sa marfi wanda zai rufe iya kan ruwan (tsarin madambaci).
3. Sai ki zuba tsakin ki a tukunyar dambun ko ki dauko buhu mai kyau ki zuba wannan tsakin, sannan ki sa a cikin tukunyarki, ki rufe ya turara.
4. Idan ya turara sai ki fito dashi ki juye a roba mai kyau, ki jajjaga attarugu ki zuba sai ki yanka albasa ki sa a ciki, ki sa maggi, da gishiri, da kayan kanshi, da gyada, da zogale, ki juyasu sosai.
5. Sai ki mayar cikin buhunki ki sa tukunya ya turara kamar minti ashirin, idan ya yi za ki ji yana kamshi.
6. Sai ki bude idan ya yi sai ki sauke.
No comments:
Post a Comment