Abubuwan da ake bukaya
* Aya
* Kwakwa
* Dabino/ko Zuma
* Sugar
* Madara
* Kayan kansh
Yadda ake hadawa
1. Ki gyara ayarki ki cire duwatsu da dattin cikin sannan ki jika a ruwa ta yini ko ta kwana amma idan za ta kwana ki tabbata kin canza ruwan gudun kada ya yi tsami
2. sannan ki cire kwallon cikin dabino ki jika dabinon tsaowon minti 30
3. Ki yayyanka kwakwarki kanana
4. Kiwanke ayar ki zuba ki zuba kwakwa da dabino a kai ki nika a blender ko ki kai inji a markado miki ita
5. Bayan kin markada sai ki tace da kyallen tata akalla sau biyu, sannan ki zuba sukari da flavor da Zuma (idan da ita ki ka yi amfani ba dabino ba) ki sa kankara
6. Idan anzo sha kuma sai a zuba madara ta ruwa ko ta gari
Shi kunun aya baya son zafi ko waje mai zafi da zaran yayi zafi to zai yi yauki, sai a
bar shi a kankara ko a saka ta a firji. Kuma ba a yinsa a ajiye ya dade
No comments:
Post a Comment