Thursday, 17 May 2018

Asha ruwa lafiya.... AWARAR KUSKUS

RAMADAN KAREEM

Ku kasan ce da filin mu a kullum don canjawa mai gida sabon buda baki mai saukin kashe kudi.
AWARAR COUSCOUS
(COUSCOUS CAKE)


 ABUBUWAN DA AKE BUKATA
* couscous
* Kwai
* Albasa da Attaruhu
* Abin dandano
* kayan kanshi

YADDA AKE HADAWA
1. Zaki jika couscous da ruwan sanyi daidai yadda zai shanye kan sa har tsahon minti 30 za ki ga ya tsotse ruwan da ki ka jika shi,
2. sai kisa yankakken albasa, dakakken tarugu, Kayan kanshi da abin dandani,
sai ki fasa kwai ki hada ki cakuda sosai,
3. sannan ki kulla a leda ki dafa kaman alale ,
4. In yayi sai ki yayyanka kaman awara sai ki kada danyan kwai ki dinga tsomawa a cikin kwan kina  soyawa a mai. aci dadi lfy

Sunday, 6 May 2018

MIYAR GARIN WAKEN SUYA

Abubuwan da ake bukata
* Waken suya
* Koda da hanta
* Busasshen kifi
* Kayan miya
* Alayyahu
* Thyme
* Curry
* Tafarnuwa
* Man ja

Yadda ake Hadawa
Ki kai waken suya a markada miki a inji, ki yanka koda da hanta ki
wanke ki tafasa ta da thyme, tafarnuwa, gishiri da albasa, ki dora manki
a wuta, idan yayi zafi sai ki zuba markadadden kayan miyarki a kai,
idan ya soyu kamar minti sha biyar sai ki kwaba garin waken suyarki
da ruwa, ki zuba akan kayan miyar ki zuba koda da hanta, kisa maggi
da gishiri da curry, idan yayi kamar minti goma sha biyar yana dahuwa
sai ki zuba busasshen kifinki da kika gyara kika wanke, ta kuma
dahuwa kamar minti goma ko sha biyar, za ki iya zuba alayyahu idan
kina so, kuma za ki iya barinta haka ba sai kinsa alayyahu ba, zaki iya
yiwa maigida da shinkafa, ko tuwon shinkafa, ko taliya ko eba.

Sunday, 29 April 2018

KUNUN MADARA DON BUDA BAKI....


SANARWA.....  DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMIDUMINSU SAI A SHIGA. https://www.alkaryarhausa.blogspot.com

 Abubuwan da ake bukata

1. Madarar gari
2. Danya ko busashsshiyar citta (a daka/kirba)
3. Fulawa
4. Lemon tsami
5. Dafaffiyar alkama ko shinkafa
6. Sikari da yar zuma
7. Kaninfari da citta mai yatsu (a daka)

Yadda ake Hadawa

* Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba kaminfari da citta a ciki sai ki
bari ya tafaso
* Idan ya tafasa sai ki kawo dafaffiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya
* Sai ki kawo fulawa ki kwabata da ruwa ki ringa zubawa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
* Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki
* Sai ki zuba sikari da yar Zuma in kina bukata a sha

Thursday, 12 April 2018

MIYAR KABEJI


Abubuwan da ake bukatar

• Kabeji
• Nama
• Man gyada
• Attarugu
• Albasa
• Tumatir
• Magi
• Kori
• Tafarnuwa

Yadda ake Hadawa
Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka  manya-manya sannan a
wanke da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki
sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga
attarugu da tafarnuwa.
Daga nan sai wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan
bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama.
Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a
zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya.
Sannan a dauko naman a zuba ba tare da romon ba. A zuba magi da
kori a gauraya a jira su tafasa sau daya sannan a zuba kabejin a
gauraya a dan rufe. Bayan mintuna biyu, sai a sake budewa a gauraya
sannan a rufe na tsawon mintuna uku sannan a sauke.
A dora a kan shinkafa dafa-duka zazzafa ko kuma farar shinkafa da
makamancinsu. A ci dadi lafiya!

Saturday, 7 April 2018

MIYAR SHUWAKA



Abubuwan da ake bukata
1. Makani
2. Ganyen shuwaka
3. Naman sa da kaza da kayan ciki da harshen sa da busashshen kifi
4. Daddawa
5. Attaruhu da tattasai
6. Man ja
7. Dakakken karafish
8. Gishiri da dunkulen knorr
9. Albasa

Yadda ake hadawa

1. Ki wanke kayan ciki sosai da harshen sa, ki yanka albasa da gishiri da dunkulen knorr ki zuba akai, ki zuba ruwa ki rufe ki dora akan wuta.
2. Kayan ciki yana da daukar lokaci kafin ya dahu. Idan kuma kina da (pressure cooker) shi kenan, nan da nan za ki ga ya dahu.
3. Busashshen kifinki kuma ki wanke sosai ki tsame ki ajiye a gefe daya.
4. Ki dafa nama da kaza, shi ma ki yanka albasa, ki zuba gishiri da dunkulen knorr. Amma daban-daban za ki dafa su, domin kaza ta fi nama saurin dahuwa musamman idan naman sa ne. Ka da ki zuba ruwa da yawa, kadan din ruwan naman da zaki samu ya fi mai yawa din nan. Sai dai idan kin ga naman bai dahu ba kina iya kara ruwa .Saboda kadan din ya fi zaki da amfani a jiki.
5. Idan naman ya kusa dahuwa sai ki zuba busashshen kifin da ki ka wanke su karasa dahuwa tare. Ki wanke makaninki ki dafa shi a cikin ruwa, idan ya dahu sai ki sauke ki bare
bawon ki daka shi a turmi. Idan kuma kina da dan karamin injin nika wato (blender) sai ki zuba shi a cikin (blender) ki zuba ruwa. Amma ki dan marmasa makanin da hannu saboda ya yi saukin nukuwa a cikin blender din.
6. A cikin babbar tukunya ki kawo kayan cikin da harshen sa da busashshen kifi da kaza da nama da kika dafa ki zuba a cikin babbar tukunya, ki kawo markadadden tattasai da attaruhu ki zuba akai, ki zuba manja da daddawa da gishiri da dunkulen knorr ki juya, ki barshi kamar minti biyar zuwa minti takwas. Idan kika ji kamshin daddawar ya fara tashi sai ki zuba wannan makanin da kika nika, da farko za ki ga ya fara tashi , idan ya yi ‘yan mintuna kuma sai ki ga ya ,lafa ya fara yauki.
7. Ki juya sosai ki kawo karafish ki zuba a ciki. Karafish yana saka miya ta yi kauri. Idan kin ga miyar ta yi kauri sai ki kara ruwan nama, idan kumabaki da shi kina iya kara ruwa. Wasu suna son miyar shuwakarsu da kauri a yayin da wasu suke sonta da ruwa-ruwa. A gefe kuma kin riga kin wanke shuwakarki sosai da ruwan zafi , idan baki son dacinta da yawa sai ki dafata da kanwa da gishiri, dacin zai ragu sosai, idan ba haka ba kuwa sai kiyi ta wanke shuwakar har sai ta daina wannan kumfa-kumfar kuma koren ya ragu. Ki yankata yadda kike so, wasu suna son su yanka ganyen da girma domin suna jin dadin taunawa, yayin da wasu kuma suke yanka ganyen kananu sosai.
8. Ki rage wuta sosai ki zuba ganyen shuwakar a ciki, ki bar ganyen ya dahu. Ganyen shuwaka ya fi alaiyahu tauri, saboda haka ki bar shi zuwa minti takwas ko goma. Idan kin ga ya yi kauri da yawa sai ki kara ruwa. Ki dandana ki ji komai ya ji.

Wednesday, 4 April 2018

MIYAR EDIKA IKONG

Abin Sani

Miyar Edikan Ikong ba miyar Hausawa ba ce, sai dai miya ce da
al’ummar Hausawa ya kamata ta mika hannu ta karba, ta runguma
saboda armashin miyar a baki da kuma dimbin alfanunta ga lafiya.
Miyar Edikang Ikong miyar kabilar Efik ce. Ita kuwa kabilar Efik
tushensu na jihohin Cross River da Akwa Ibom a kudancin Nijeriya.
Su ne kabilar da ake kira da Calabar saboda wani adadi mai yawa na
Efik sun fito ne daga garin Calabar, babban birnin jihar Cross River. Ga
dai yadda ake shirya miyar ta Edikang Ikong:

Abubuwan da ake bukatar

* Alayyahu
* Ganyen Ugu
* Ganyen Gurai (water leaves)
* Manja
* Naman sa
* Ganda
* Kayan ciki
* Cray fish
* Hanta
* Busasshen kifi
* Albasa
* Attaruhu
* Gishiri
* Sinadarin Dandano
* Curry
* Thyme
* Citta da sauran kayan kamshi
* Fafarnuwa

Yadda Ake Girka Miyar Edikang Ikong

1. Za ki sami tukunya, ki zuba, namanki, da gandarki, da kayan ciki (bayan kin wanke su da kyau). Ki sa musu albasa isasshe, da thyme, curry, da sinadarin dandano da gishiri, citta, da tafarnuwa. Ki zuba wadataccen ruwan da zai dafa su, ki aza bisa wuta ki barsu su
dahu sosai. Bayan kin tabbatar da dahuwarsu
2. Sai ki sami busasshen kifinki, ki wanke shi tsaf,  wurin wankewar ki dan saka gishiri, bayan kin yi wankewar farko, sai ki saka masa ruwan zafi sannan ki tsane shi, sai ki
sa a cikin naman ki da ya dahu, ki bar shi ya yi kamar minting 8.
3. Bayan ruwan tafasan namanki ya yi kasa sosai, don miyar ba a cika wa miyar Edikang Ikong ruwa, sai ki zuba jajjagaggen taruhu, cray fish, da kuma manja, sa’annan ki jujjuya, sai ki barshi ya dahu na kamar minti 5, sannan ki saka sinadarin dandano.
4. Sai ki dauko ganyen alayyahunki da na water leaves da tuni dama kin yanka kin wanke kin kuma tsane, ki zuba akan hadin miyar. Sai ki tona miyar ta yadda ganyen da kayan hadin za su hautsina sosai, sai ki barshi na ‘yan mintina.
5. Bayan ‘yan mintina sai ki zuba ganyen Ugunki, ki jujjuya, zaki ga miyan duka ya kame babu ruwan miya a cikin sa sai dan kadan, sai ki dan bashi mintina ki rage wutan yadda ganyen za su turaru.
6. Sai ki sauke, Za a iya ci da Sakwara, tuwo, teba, farar shinkafa da dai sauransu

A lura: Za ki iya dafa gandarki daban tunda shi yana da tauri, wasu kuma suna tafasa dukkan naman da zasu yi amfani dashi. Miyar bata bukatar kayan miya kamar yadda muke yin miyarmu, taruhu 3 zuwa 5 ya isa. Sannan miya ce da ke da bukatar nama isasshe. Miya ce mai mutukar kara lafiya saboda ganyayykin da aka yi amfani da su.

Monday, 2 April 2018

MIYAR WAKE

Abubuwar da za a bukata
• Wake
• Man ja
• Attarugu
• Busasshen kifi
• Albasa
• Gishiri da magi

Yadda ake Hadawa

1. Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika, idan ya jiku sai ta cire hancin jikin waken.
2. Sai ki daura ruwa a wuta, idan ya tafasa sai ki zuba waken ya yi ta tafasa har sai ya nuna ya yi lugwi.
3. Sannan sai ki zuba yankakkiyar albasa da dakakken attaruhu da manja da busasshen
kifi. Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na mintuna kadan,
4. Sannan sai a zuba magi da gishiri a rude tukunya zuwa Karin mintuna 3 zuwa 5, sai a sauke! Ana iya cin wannan miyar ne da tuwon shinkafa. Kuma anfi son amfani da ita da rana ko da yamma.

Wednesday, 28 March 2018

KUNUN MADARA

Abubuwan da ake bukata

1. Madarar gari
2. Danya ko busashsshiyar citta (a daka/kirba)
3. Fulawa
4. Lemon tsami
5. Dafaffiyar alkama ko shinkafa
6. Sikari da yar zuma
7. Kaninfari da citta mai yatsu (a daka)

Yadda ake Hadawa

* Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba kaminfari da citta a ciki sai ki
bari ya tafaso
* Idan ya tafasa sai ki kawo dafaffiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya
* Sai ki kawo fulawa ki kwabata da ruwa ki ringa zubawa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
* Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki
* Sai ki zuba sikari da yar Zuma in kina bukata a sha

Tuesday, 27 March 2018

EGG PIZZA

Abubuwan da ake bukata

1. Danyan Kwai
2. Dankalin turawa
3. Attaruhu
4. Tattasai
5. Albasa
6. Koren tattasai
7. Koren wake
8. Jar masara (Danya) 
9. Karas
10. Maggie,
11. Kayan kamshi da curry d.s
12. Mai

Yadda ake hadawa

1. Ki feraye dankalinki ki yi ma sa yankan cube (kusurwa shida) kanana kanana sai ki soyashi sama sama da dan gishiri kadan sai ki ajeshi gefa

2. Ki yayyanka kayan miyarki da aka lissafo (Attaruhu, tattasai, Koran tattasai da Albasa) suma ki soyasu da dan mai kadan (karamin cokali)  ma ya isa sai ki sa karas da masararki da kayan kamshi ki ci gaba da soyawa sama sama, ki sauke ki ajiye

3. Sai ki dauko soyayyen dankalinki ki hadasu wuri guda ki cakuda su hadu

4. Sai kifasa kwai ki zuba a Kansu sai kisa a oven, kar asa wuta da yawa don zai kone

5. da kinji yafara kamshi sai ki duba ki gani in ya yi sai ki juye a tire mai fadi dai dai fadinshi
shikenan saiki yayyanka.

Sai a duba sababbun shafukan mu..

https://www.alkaryarhausa.blogspot.com

https://www.taskarannashuwa.blogspot.com

Monday, 26 March 2018

KUNUN SHINKAFA

Abubuwan da ake bukata

. Kwakwa (dai-dai misali)
2. Shinkafar tuwo
3. Madarar ruwa
4. Suger
5. Kayan kamshi
6. Flavor (in kina bukata)

Yadda ake hadawa

1. Ki wanke shinkafar ki ki jikata kamar awa 2 kiwanke ki zuba kayan kamshi ki bayar a markadota a inji sai ki tace ta da yankin tata kamar kullin koko, ki bar ruwan ya kwanta ya yi gasara
2. Ki kankare bayan kwakwar ki saiki wanke ta sai ki goga ta
da grater ki raba ta gida hudu (4) ki dau kashi daya (1) ki aje a gefe, ki markada sauran kashi ukun (3) a blander ko ki kirba a turmi, ki tace ruwan kisa ruwan kwakwar daidai yawan kunun da zaki yi ki dora ruwan kwakwar a kan wuta
3. Idan ruwan kwakwar ya tafasa ki sauke ki dauko tafashasshan ruwan kwakwar ki sheka/kwara cikin kullin shinkafar ki dama sai ki dauko sauran gogaggiyar kwakwar nan ki zuba ki juya
4. Ki zuba sugar da madarar ruwanki da flavour (in kina da bukata) ki juya sosai.

KUNUN AYA

Abubuwan da ake bukaya

* Aya
* Kwakwa
* Dabino/ko Zuma
* Sugar
* Madara
* Kayan kansh

Yadda ake hadawa

1. Ki gyara ayarki ki cire duwatsu da dattin cikin sannan ki jika a ruwa ta yini ko ta kwana amma idan za ta kwana ki tabbata kin canza ruwan gudun kada ya yi tsami
2. sannan ki cire kwallon cikin dabino ki jika dabinon tsaowon minti 30
3. Ki yayyanka kwakwarki kanana
4. Kiwanke ayar ki zuba ki zuba kwakwa da dabino a kai ki nika a blender ko ki kai inji a markado miki ita
5. Bayan kin markada sai ki tace da kyallen tata akalla sau biyu, sannan ki zuba sukari da flavor da Zuma (idan da ita ki ka yi amfani ba dabino ba)  ki sa kankara
6. Idan anzo sha kuma sai a zuba madara ta ruwa ko ta gari

Shi kunun aya baya son zafi ko waje mai zafi da zaran yayi zafi to zai yi yauki, sai a
bar shi a kankara ko a saka ta a firji. Kuma ba a yinsa a ajiye ya dade

Saturday, 24 March 2018

KUNUN ALKAMA NAU'I NA BIYU (2)

Abubuwan da ake bukata


1. Alkama (gwangwani 4)
2. Gyada (Gwangwani 1½)
3. Aya ((Gwangwani 1)
4. Farar shinkafa (Gwangwani 1½ in ana bukata)
5. Suga ko Zuma (in ana bukata)
6. Kayan kamshi
7. Madara/Nono/Yoghurt (in ana bukatar karin armashi)

Yadda ake Hadawa

1.Za ki wanke alkama, shinkafa da ayar ki, ki shanya su su bushe, ki gyara gyada, sai a hada da kayan kamshi akai a niko a tankade (an hada barin kunun alkama ke nan
2. Ki daura ruwa a wuta
3. Sai ki debi garinki yanda zai miki saiki kwaba kamar zakiyi talgen tuwo,
4. In ruwan ya tafasa sai kibdama kibarshi a kan wutar amma ki rage wutar zuwa minti 2-3, sai kisauke,
5. A sa sugar ko zuma da madara ko yoghurt sai a sha.

Wannan shi ne nau'i na biyu

KUNUN ALKAMA NAU'I NA DAYA


Abubuwan da ake bukata

1. Alkama (Gari kofi 1½, kura kura ½ kofi)
2. Fadar shinkafa (¼ kofi)
3. Gyada Markadadde (¼ kofi)
4. Kayan kamshi
5. Suga
6. Nono (Kindirmo ⅓ kofi)

Yadda ake hadawa

1. Ki wanke alkamarki da farar shinkafa ki sa a tukunya ki dora a wuta, ki dafa
2. Sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki dora ruwan gyada a wuta, ya tafasa
3. Idan ya tafasa sai ki dauko dafeffiyar alkamarki da shinkafa ki zuba ki
barshi ya kara nuna.
4. Sai ki dama garin alkamarki ki sa kayan kamshi ki juya
5. Idan ya juyu sai ki sauke tukunyar ki a kasa ki zuba damammen garinki dama
sosai.
6. Sai ki zuba suga da nono ki juya sosai.

Wannan shi ne nau'i na farko

Friday, 23 March 2018

ALKUBUS

Abubuwan da ake bukata:

* Flour gwan gwani 2
* Garin Alkama gwangwani 1
* Yeast cokalin shan shayi
* Ruwan kanwa dan kadan (rabin cokalin shan shayi)
* Gishiri dan kadan
* Mai dai dai misali

Yadda ake hadawa

1. Ki hada garin flour da na alkama ki tankade a roba,
2. ki jika yeast da ruwan zafi, ki hada da gishiri kadan idan kina so,
3. Sai ki kwaba garinki da ruwan yeast din, da tauri za ki yi kwabin yafi na funkaso, ki ajiye a wuri mai dumi (cikin daki ko store in da ba fanka ko A.C) awa hudu zuwa shida zai kumburo, 4. Sai ki zuba ruwan kanwa kadan da mai kadan kiyi ta bugawa ya bugu sosai yadda zai tashi, kuma ya bugu sosai,
5. sai ki zuba a gwangwanayen alala bayan kin shafa mai, ko kananan kwanuka, ko ki kulla a leda, (idan kina so za ki iya barbada kantu a sama bayanin kin sa a gwangwanaye don kwalliya da dadin armashi)
6. sai ki dora a tukunya ki turara, da madambacci ko tukunyar dambu, idan yayi za ki
ji yana kamshi.
7. Sai a sauke a naimi miya mai kyau a ci cikin nishadi da walwala....

Thursday, 22 March 2018

TARBIYYA NA FARAWA DAGA GIDA

Matsaloli da illolin da sakaci da tufa/suturar da mata ke sawa Suna da matukar illa da tasiri a cikin al'umar bahaushe da musulunci a wannan zamani......

Abin tambaya:-

1. Mai ya sa a ke suturce yaya maza daga sama har kasa? Amma
2. Me ya sa ake suturce yaya mata rabi-da-rabi tun suna yara?
3. Mai ya sa ake anfani da kwalliya da da tsiraicin mata don cimma wata bukata/manufa?

Wannan a kan ku/mu ya ke gaba daya
-iyaye mata
-kakanni mata
-yayye mata
-masu kula da gida mata

Ya kamata mu kula mu canza dabi'un mu, duk abin da ya wuce ko aka yi a baya ya kamata ya zaman darasi... Gyaran Al'umma ya na kan mu gaba daya

Wednesday, 21 March 2018

KUNUN GYADA


KUNUN GYA‘DA (NA NI‘KA)

Abubuwan da ake bukata:

1. Gero
2. Citta (mai yatsu)
3. Barkwano
4. Tsamiya/lemon tsami
5. Gyada
6. Sukari/sugar ko Zuma

YADDA AKE HADAWA

1.Gyara geronki (a wanke a rege tsakuwa) kisaka citta (mai yatsu) da barkwano kaddan, kibayar aniko miki.
2. Dauko rariyar ki kitankade.
3. Jika tsamiya dan kaddan, ki tace ruwan tsamiyan, inkuma lemon tsami ne kiyanka, kimatse ruwan saiki tace.
4. Debi tankadedden garin geronnan daidai wanda zai mi ki, kidebo ruwa kizuba ki gauraya (kaurin yayi daidai kaman na gasarar talge), sai ki dauko ruwan tsamiya/lemon tsamin nan kizuba akai.
5. Ki debi gasaran dakika daman nan dan kadan akofi sai ki ajiye su agefe/rufe
6. Soya gyadar ki sama sama ki murje ki bushe ta ki bayar amarkado miki, sai ki kara ruwa akai kitace sai ki ajiye taceccen ruwan gyadar agefe ki rufe.
8. Tanadi sukari/sugar ko zuma (ga
mai bukata).
9. Ajiye ludayinki wankakke akusa.
10. To uwar gida, hura wuta ki daura tukunyar ki, dauko taceccen ruwan gyadan kin nankizuba a tukunyar.
11. Ki bar wutar tana ci (zai taso ya yi kumafa ya yi kamar zai zuba, to sai a kula, sai a sa ludayi a dinga juya wa..
12. In ruwan gyadar ki ya tafasa, sai a sauko dashi daga kan wuta ki juye akan gasarar geron nan (mai yawan) ki ringa juyawa.
13. Bayan minti kaman 5, sai ki dauko waccan gasarar da ki ka diba (a kofi) sai ki zuba akan mai zafin nan ki juya.
14. Dauko sukari (sugar) ko zumar ki ki zuba (gamai bukata)...

AKULA:

WURIN TACE MARKADADDIYAR GYADAR NAN KAR ASA RUWA SOSAI, DON IN RUWA YAYI YAWA TO FA UWAR GIDA KUNUN KI BA ZAI YI GARDIN GYADA BA KUMA BA ZAI YI MIKI
HASKE BA. SANNAN TSAMIYA/LEMON TSAMIN KAR YAFITO (DAN KADAN ZAKI ZUBA) DON AKWAI WADANDA BASU DA BUKATAR TSAMI/ZAKI. ZA‘A IYA SURFA GERON KAFIN AYI KUNUN, AMMA! AYI DA DATSA (WANDA BA‘A SURFABA) KUNUN YAFI DADI DA KARA LAFIYA BAKI.

DAMBUN MASARA

Abubuwan da ake bukata

1. Tsakin Masara (barjajjiyar masara)
2. Zogale ko Alayyaho
3. Attaruhu
4. Albasa
5. Man gyada
6. Dakakkiyar gyada
7. Maggi
8. Kayan kanshi
9. Gishiri

Yanda ake hadawa
1. Da farko uwargida za ki wanke tsakin masararkii ya fita tas, sai ki tsane shi a mararaki.
2. Idan ya tsane sai ki zuba ruwa a tukunyar dambu ko tukunya mai dan zurfi,  sai ki sa marfi wanda zai rufe iya kan ruwan (tsarin madambaci).
3. Sai ki zuba tsakin ki a tukunyar dambun ko ki dauko buhu mai kyau ki zuba wannan tsakin, sannan ki sa a cikin tukunyarki, ki rufe ya turara.
4. Idan ya turara sai ki fito dashi ki juye a roba mai kyau, ki jajjaga attarugu ki zuba sai ki yanka albasa ki sa a ciki, ki sa maggi, da gishiri, da kayan kanshi, da gyada, da zogale, ki juyasu sosai.
5. Sai ki mayar cikin buhunki ki sa tukunya ya turara kamar minti ashirin, idan ya yi za ki ji yana kamshi.
6. Sai ki bude idan ya yi sai ki sauke.

Monday, 19 March 2018

MIYAR WAKE

Yadda ake miyar Wake

Abubuwan da ake bukata
1. Wake
2. Manja
3. Attarugu
4. Bushenshen kifi (banda) a sa ruwan zafi a wanke
5. Albasa
6. Maggi
7. Kayan kamshi
8. Nama (Karin armashi) a tafasa da albasa da kayan kamshi
9. Tafarnuwa
10. Gishiri

Yadda ake hadawa
1. Da farko dai zaki wanke wakenki ya fita sosai
2. Sai ki dora ruwan ki a wuta ya tafasa, sai ki zuba wakenki ya
yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi lukwui
3. Sai ki zuba jajjagaggen attaruhu, da albasa, da manja, da
kifinki da tafashasshen namanki sai ki jira ruwan miyarki har sai ya tatafasa. Za ki ji yana
kamshi
4. Sai ki zuba maggi, da kayan kamshi, da tafarnuwa, da gishiri,
sai ki barshi kamar minti sha biyar za ki ji gida ya dau kamshi
5. Da zarar kin duba miyarki tayi shikenan sai ki sauke
6. Zaki iya cin miyarki da tuwon shinkafa ko masara ko
semonbita. Ko ma da breadi ko gurasa

DAN WAKE

Yadda ake yin danwake
1. Farkodai za'a jika kanwa
2. Sannan A samu garin fulawa ko garin rogon danwake a tankade
3. Sai a tankade kuka 'yar kadan a hada da wannan tankadadden garin atonasu gaba daya
4. Sai akawo waccan jikakkiyar kanwar a zuba a kai
5. Sai a tona har su hadu
6. Sannan asamu tukunya mai kyau a dora akan wuta har sai ya tafasa
7. Sai arinka diban wancan kwabbben kullun ana gutsurar daidai gwargwadon yadda akeso ana jèfawa cikin wannan tafasasshen ruwan
8. Idan aka gama sai a bar shi yayi ta tafasa. ana yi ana juyawa, a bashi dan lokaci kadan
9. Daga nan sai a rika tsamewa ana zubawa acikin wani ruwan daban mai sanyi ko mai dumi 10. Sannan a samu abin soya azuba man gyada ko man ja, sai a yanka 'yar albasa aciki a soya
11. Idan ya soyu a kwashe.
12. Tuni daman an tanadi dakakken yaji, maras daddawa
13. Sai a kwashe danwaken, a tsane shi, sannan a zuba shi a kwano wankakke.
14. Sannan a bade shi da yajin nan, kuma a dan bar bada gishiri ko marmasa magi.
15. Daganan kuma sai a zuba wannan soyayyen man
16. Shikenan danwake ya hadu, a ci atsanake da tsinke ko cokali mai yatsu mai kyau